Isa ga babban shafi
Iraqi

Kotun Iraqi ta yanke wa Hashemi hukuncin kisa

Wata Kotu a kasar Iraqi, ta yankewa mataimakin shugaban kasar, Tariq Hashemi, hukuncin kisa, bayan samun shi da laifin mallakar kungiyar ‘Yan-ina-da-kisa, a wata shari’ar da aka masa a bayan idonsa.

Tareq al-Hashemi lokacin da yake zantawa da kamfanin Dillacin labaran Reuters
Tareq al-Hashemi lokacin da yake zantawa da kamfanin Dillacin labaran Reuters REUTERS
Talla

Hukuncin na zuwa ne bayan samun jerin hare hare a sassan yankunan kasar Iraqi wadanda suka yi sandiyar mutuwar mutane 92.

Mista Hashemi, shi ne babban jami’in gwamnati daga bangaren mabiya Sunni a kasar Iraqi, wanda ke karkashin jagorancin mabiya Shi’a, da ake zargi da musguna masa.

Mataimakin shugaban kasar, wanda jiya ya gana da jami’an gwamnatin Turkiya, ya ki cewa komai game da hukuncin, sai dai magoya bayansa sun soki shugaban kasa, Nouri al Maliki, da yi masa bita da kulli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.