Kotun Iraqi ta yanke wa Hashemi hukuncin kisa - Asiya - RFI

 

Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h30 GMT
  Labarai 04/10/2015 06:00 GMT
 • 07h00 - 07h30 GMT
  Labarai 04/10/2015 07:00 GMT
 • 16h00 - 17h00 GMT
  Labarai 04/10/2015 16:00 GMT
 • 20h00 - 20h30 GMT
  Labarai 04/10/2015 20:00 GMT

Asiya

Kotun Iraqi ta yanke wa Hashemi hukuncin kisa

media Tareq al-Hashemi lokacin da yake zantawa da kamfanin Dillacin labaran Reuters REUTERS

Wata Kotu a kasar Iraqi, ta yankewa mataimakin shugaban kasar, Tariq Hashemi, hukuncin kisa, bayan samun shi da laifin mallakar kungiyar ‘Yan-ina-da-kisa, a wata shari’ar da aka masa a bayan idonsa.

Hukuncin na zuwa ne bayan samun jerin hare hare a sassan yankunan kasar Iraqi wadanda suka yi sandiyar mutuwar mutane 92.

Mista Hashemi, shi ne babban jami’in gwamnati daga bangaren mabiya Sunni a kasar Iraqi, wanda ke karkashin jagorancin mabiya Shi’a, da ake zargi da musguna masa.

Mataimakin shugaban kasar, wanda jiya ya gana da jami’an gwamnatin Turkiya, ya ki cewa komai game da hukuncin, sai dai magoya bayansa sun soki shugaban kasa, Nouri al Maliki, da yi masa bita da kulli.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure