Al’ummar Iraqi suna zaman makoki bayan mutuwar mutane 111
Al’umomin Kasar Iraqi, sun shiga juyayin rasa dimbin rayukan jama’ar kasar da aka yi a jiya Litinin, sakamakon wasu jerin haren haren da ba a taba ganin irinsu ba, a cikin shekaru biyu da suka gabata, da suka hallaka mutane 111.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumomin kasar sun ce, mutane 235 suka samu raunuka, a hare haren 28, da aka kai birane 19, wanda ya janyo suka daga sassan duniya.
Wadannan ne hare hare mafi muni da aka kai a kasar Iraki a dai dai lokacin da al’ummar Musulmi ke gudanar da Azumin watan Ramadan.
Hare haren na zuwa ne kwana daya bayan kai wani harin Bom da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 17.
Jami’an kiwon Lafiya sun ce akwai mutane 18 da suka mutu a birnin Taji inda kuma mutane 29 suka jikkata.
Da misalin karfe Biyar na safiyar Litinin kuma wasu ‘Yan Bindiga suka kaddamar da hari a sansanin Soji da ke Albu Slaib da ke Gabas da birnin Dhuluiyah, inda suka kashe dakarun Sojin Iraki Bakwai.
Akwai wasu Jerin hare haren bama bamai da aka kai a Birnin Bagadaza da kuma wasu Birane da ke makwabtaka da birnin.
Har yanzu dai babu wadanda suka fito suka yi ikirarin daukar nauyin kai hare haren amma a kwanan baya kungiyar al Qaeda ta yi gargadin karbe ikon kasar Iraki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu