Isa ga babban shafi
Syria-MDD

‘Yan adawar Syria sun yi kiran wata sabuwar zanga-zanga

‘Yan adawa a Syria sun yi kiran hada wata sabuwar zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad bayan kammala sallar Juma’a a wani matakin farko na saba yarjejeniyar tsagaita wuta ta Kofi Annan mai Shiga tsakanin rikicin kasar.

Har yanzu dakarun Syria suna yankunan 'Yan adawa
Har yanzu dakarun Syria suna yankunan 'Yan adawa
Talla

Wannan yana zuwa ne bayan dakarun gwamnati sun sake kaddamar da hare hare da yammacin Alhamis a yankunan ‘yan Adawa.

Gwamnatin Syria ta yi kunnen uwar shegu da bukatar janye dakarunta a yarjejeniyar sansata rikicin kasar da Kofi Annan ya tsara don kawo karshen boren da aka kwashe shekara ana yi da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 9,000.

Wayewar safiyar Alhamis Maishiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Anan, yace a karon farko an samu dakatar da buda Wuta a kasar ta Syria kasancewar gwamnatin kasar da masu adawa da ita na kokarin karbar shirin sa na samar da zaman lafiya.

Sai dai Kofi Annan yace ya lura shugaba Basharul-Asad, bai goyi bayan tsarin majalisar Dinkin Duniya ba, inda ya yi kira ga Kwamitin tsaro ta bukaci janye daukacin Sojojin kasar daga inda ake tafka rikici, tare da komawa a Barikokin su.

Sakataren majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi kira ga kasar Syria akan ta aiwatar da dukkanin shirin majalisar na samar da zaman lafiya a kasar a matakai shida da Kofi Annan ya tsara. Tare da yin kira ga ‘yan adawa akan su sa wukar su kube, tare da kai zuciya nesa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.