Isa ga babban shafi
Syria

An samu sassaucin rikici a Syria, inji masu sa ido

Masu sa ido a rikicin Syria sun ce an samu sassaucin rikici a kasar, bayan cim ma wa’adin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta. An samu sassaucin daga bangaren gwamnati da ‘Yan Tawaye.

Wasu yara a Sansanin 'Yan gudun Hijirar Syria a Turkiya
Wasu yara a Sansanin 'Yan gudun Hijirar Syria a Turkiya © Umit Bektas/Reuters
Talla

Masu sa ido a kasar sun ce wa’adin ya kawo karshe ba tare da samun wani rikici ba da safiyar Alhamis.

Da safiyar Alhamis ne wa’adin ya kawo karshe Karkashin yarjejeniyar da Kofi Annan ya tsara domin sasanta rikicin kasar.

Sai dai har yanzu babu tabbacin ko hakan zai iya kawo karshen zubar da jini a cikin kasar bayan kwashe fiye da shekara ana yaki tsakanin gwamnati da masu adawa da Shugaba Assad.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 9,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.