Isa ga babban shafi
Maldives

Manbararren Shugaban kasar Maldives Nasheed ya yi watsi da kafa gwamnatin hadaka

Manbararren Shugaban kasar Maldives Mohamed Nasheed yau Lahadi ya yi watsi da kirar da Amurka tayi, na neman cimma matsaya, domin kafa gwamnatin hadin gwiwa, saboda kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Talla

Nasheed ya dage cewa juyin mulki akayi masa wajen tilasta masa murabus, inda ya shaida wa magoya bayansa a Male babban birnin kasar cewa jam’iyyarsa zata nemi gudanar da zabe cikin gaggawa. Kuma ba zasu amince da kafa wata sabuwar gwamnati ba. An watse daga taron lami lafiya.

Kasar Amurka ta nemi sabon Shugaban kasar Mohamed Waheed ya kafa gwamnatin hadin gwiwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.