Isa ga babban shafi
Iraqi

Gara Saddam Hussain da Maliki, inji Masu Sharhi

A jiya Alhamis ne wasu jerin bama bamai guda 14 suka tashi a birnin Bagadaza da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 67. Kuma hare haren na zuwa ne cikin rudanin siyasa tsakanin Fira Ministan kasar Nouri al Maliki mabiyi Shi’a da shugabannin Sunni, rikicin da ke kokarin raba Iraqi gida biyu.

Nouri al-Maliki Fira Ministan kasar Iraqi
Nouri al-Maliki Fira Ministan kasar Iraqi Wathiq Khuzaie /Getty Images
Talla

Tarek al-Homayed, Editan Jaridar Arsharq al-Awsat ya danganta Fira Ministan kasar Naouri al-Maliki matsayin mai tsattsauran Ra’ayi fiye da tsohon shugaban kasar Sadam Hussian.

Sai dai ba Homayed ba ne mutum na fark0 wanda ya fara wannan tsokacin, ko a farkon watan Disemba mataimakin Fira Ministan kasar, Saleh Mutlak Dan Sunni a wata hira da ya yi a kafar Telebijin a kasar yace gwara Saddam da Maliki.

A yanzu haka dai ana zaman doya da manja ne tsakanin mabiya Shi’a da ‘yan Sunni wanda hakan ke kokarin gurgunta gwamnatin hadin gwiwar da aka girka shekaru 10 da suka gabata.

Mataimakin shugaban kasar Tariq al Hashemi wanda gwamnatin kasar ta bada sammacin kamo shi, ya zargi Maliki game da hurar wutar rikicin kasar.

A cewarsa ya dace Maliki ya mayar da hankali wajen samar da tsaro a kasar sabanin tarwatsa ‘yan siyasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.