Isa ga babban shafi
Faransa

An kawar da barazanar cutar Cholera a Faransa

Hukumomin a Faransa sun baiyana kawar da barazanar cutar Cholera da aka yi zargin wani karamin yaro da ya shigo jirgin daga kasar Lageria da ita, kamar yadda majiyar asibitin jihar Oran-Perpignan, dake kudancin Faransa inda jirgin ya sauka suka sanar.

wani likita na yiwa wani yaro mai shekaru 9 da ya kamu da cutar cholera magani a cibiya MSF dake kasar Yémen, mayu 2017.
wani likita na yiwa wani yaro mai shekaru 9 da ya kamu da cutar cholera magani a cibiya MSF dake kasar Yémen, mayu 2017. Nuha Haider/MSF
Talla

A cikin wata sanarwar mahukumtan jihar sun bayyana cewa, bayan gudanar da binciken asibiti an kawar da barazanar kamuwa da cutar ta Cholera ga yaron mai shekaru 8 da ya nuna alamun da suka sa aka zargi cewa, yana fama ne da cutar ta amai da gudawa ne, bayan da jirginsa ya sauka a garin Oran-Perpignan dake kudancin Fransa a safiyar jiya talata.

Pasinjoji 150 dake cikin jirgin an umarce su da su fice daga cikin jirgin bayan da jami’an kiyon lafiya da na agaji suka dau nauyinsu sakamakon zargin yaron na dauke ne da cutar ta Kolera inda aka garzaya da shia asibiti tare da mahaifiyarsa da kuma wani makusancinsu.

Sauran fasinjojin 147 kuma an kebe su bayan tsaresu a cikin jirgin na kusan rabin awa.

Wannan zargi dai ya biyo bayan ganin jirgin ya fito ne daga kasar Aljeriya kasar da cutar Cholerar ta barke tun ranar 7 ga watan ogustan da ya gabata inda mutane 74 suka kamu a yayinda 2 suka rasa rayukansu, kafin a ranar talata ministan kiyon lafiyar kasar Mokhtar Hasbellaoui ya bayyana kawo karshenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.