Isa ga babban shafi
Guinea Bissau

Sissoco Embalo ya sha rantsuwar kama aiki

Shugaban Guinea Bissau mai jiran gado Umaro Sissoco Embalo yayi rantsuwar kama aiki a jiya alhamis a dai dai lokacin da takaddama tayi zafi tsakaninsa da jagoran ‘yan adawa na jam’iyyar PAIGC Domingos Simoes Pereira, wanda tuni ya garzaya kotun kolin kasar domin kalaubalantar nasarar Umaru Sissoco.

Umaro Sissoco Embalo sabon Shugaban kasar Guinee Bissau
Umaro Sissoco Embalo sabon Shugaban kasar Guinee Bissau RFI/Charlotte Idrac
Talla

A karshen watan Disambar shekarar 2019 bara kenan a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da ya gudana, Umaru Sissoco ya lashe zaben da kashi 53.5, yayinda Periera ya lashe kashi 46 na kuri’un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Rantsuwar kama aikin Sissico da ya karbi ragama daga shugaba mai barin gado Jose Mario Vaz ya haifar da rudani a tsakanin al’ummar Guniea Bissau ganin cewar kotun kolin kasar ta bada umarnin sake kidayar kuri’un da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.