Matashi ya nemi kashe kansa a Lagas
A Najeriya, Wani matashi yayi yunkurin kashe kansa ta hanyar fadawa cikin katafaren tafkin birnin Legas dake a matsayin wutsiyar tekun Atlantic da yayi iyaka da jihar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce matashin dake cikin motar haya ta kamfanin Uber, ya bukaci direban motar ya tsaya ne akan gadar third Mainland, nan take kuma ya afka kasa cikin ruwa, sai dai yayi sa’ar tsira da ransa, bayan fadawa kan wasu itatuwa.
Wannan dai shi ne karo na 2 cikin kwanaki 10 da wani ke yunkurin kashe kansa ta hanyar fadawa cikin wutsiyar tekun dake Legas, inda kawo yanzu ba gano gawar wanda ya kunduma cikin ruwan a makon na jiya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu