Bakonmu a Yau
Shugaban kungiyar manoma da makiyayan jamhuriyar Nijar kan yarjejeniyar kiwo da Benin
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:35
Mahukunta a Jamhuriyar Benin sun bai wa makiyayan jamhuriyar Nijar damar shiga kasar domin kiwo har tsawon watanni biyu a jere, bayan da aka haramta wa makiyaya daga sauran kasashe dama shiga kasar saboda dalilai na tsaro.Jibbo Banya, shi ne shugaban babbar kungiyar da ta hada manoma da makiyaya a jamhuriyar Nijar, kuma wanda ya kasance a cikin tawagar ministan noma Abouba Albade da ta gana da mahukuntan Jamhuriyar Benin a game da wannan batu, ya kuma yiwa Sashin Hausa na RFI karin bayani yayin zantawa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.