Isa ga babban shafi
Najeriya

A Najeriya NECO ta kori ma'aikatanta 19 saboda takardun bogi

HUKUMAR Kula da jarabawar kasa a Najeriya ta NECO ta sanar da korar wasu ma’aikatan ta guda 19, watanni 4 bayan ta kori wasu 70 saboda mallakar takardar shaidar kamala karatu na bogi.

Litattafai
Litattafai ANDREY SMIRNOV / AFP
Talla

Mai Magana da yawun hukumar Azeez Sani ya ce Majalisar gudanarwar hukumar ta amince da korar wadannan ma’aikata a zaman da tayi karo na 52, sakamakon wani bincike da aka gudanar bayan gano wasu daga cikin su dake dauke da irin wadannan takardu.

Jami’in yace kafin gayyatar ma’aikatar da matsalar ta shafa, sai da Hukumar ta rubuta wasika ga makarantun da ma’aikatan suka ce sun kamala domin samun bayanai, inda suka bada shaidar cewar basu san wadannan mutane ba, kuma ba takardun su na shaida suke dauke da su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.