Isa ga babban shafi
Sahel

'Yan bindiga sun kara karfi a yankin Sahel

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, an samu karuwar hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a yankin Sahel, inda a cikin watanni 12 kadai, mutane sama da 700,000 suka tsere daga gidajensu a Burkina Faso.

Sojojin da ke yaki da 'yan bindiga a yankin Sahel
Sojojin da ke yaki da 'yan bindiga a yankin Sahel AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Rahoton Hukumar ta 'Yan Gudun Hijirar ya ce, jami’anta na fuskantar matsaloli sosai wajen kai dauki da kuma kula da bukatun 'yan gudun hijira a Sahel sakamakon karuwar hare-haren.

Hukumar ta ce, a Burkina Faso kadai, hare-haren 'yan bindigar a kan fararen hula da jami’an gwamnati na tilasta wa a kalla mutane 4,000 tserewa daga gidajensu domin samun mafaka kowacce rana, tun daga ranar 1 ga watan Janairun bana.

Hukumar ta UNHCR ta ce, ya zuwa yanzu mutane 765,000 suka tsere daga muhallansu a cikin watanni 12 da suka gabata domin kauce wa wadannan hare-hare.

Rahotan ya kuma ce 'yan kasar Nijar sama da 4,400 suka tsere daga jihohin Tillaberi da Tahoua domin samun mafaka a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.