Francophonie na fargabar zaben Guinea
Kungiyar Kasashen dake amfani da harshen Faransanci ta duniya La Francophonie ta bayyana damuwa kan shirin zaben rabagardamar kasar Guniea mai zuwa, musamman sahihancin rajistar masu kada kuri’u.
Wallafawa ranar:
Gargadin kungiyar na zuwa ne kwanaki 6 kafin zaben da za’ayi a kasar wanda Yan adawa suka bayyana a matsayin yunkurin shugaba Alpha Conde na cigaba da zama a karagar mulki.
Kungiyar tayi zargin cewar akwai matsaloli sosai a rajistar masu kada kuri’un kasar mai dauke da kusan sunaye miliyan biyu da rabi na bogi, ganin cewar kashi 98 na masu rajistar basu da takardun shaidar da za’a tantance su, yayin da wasun su sun mutu, wasu kuma basu kai shekarun kada kuri’u ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu