Isa ga babban shafi

Za a bayyana shaidar kammala karatun 'yan takara ga al'umma a Najeriya

Hukumar Zaben Najeriya ta ce za ta manna takardun shaidar kammala karatu da bayanan ‘yan takarar zaben gwamnan Jihar Edo da Ondo da za’ayi a cikin wannan shekarar domin baiwa jama’a damar tantance su da kuma gano ‘Yan takarar dake gabatar da takardun bogi.

Shugaban hukumar zaben Najeriya  Mahmood Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood Yakubu. KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images
Talla

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da kwamishinonin zabe na kasa baki daya.

Mahmud ya ce dokar zabe ta ba hukumar hurumin yin haka, saboda haka daga yanzu zasu dinga baje kolin irin wadannan bayanai ga jama’a domin baiwa masu korafi damar rugawa kotu dan kalubalantar duk wani dan takarar da ya gabatar da bayannan karya.

Shugaban Hukumar ya zargi jam’iyyun siyasa da gazawa wajen tantance ‘yan takarar da suke gabatarwa domin tsayawa zabe abinda ke haifar da zuwa kotu domin tantance wanda ya dace ya hau kujerar takara.

Mahmud ya ce za’a gabatar da sunaye da takardun shaidun ‘yan takarar Jihar Edo daga ranar 6 ga watan Yuli mai zuwa, yayin da za’a kwatanta haka a Jihar Ondo ranar 4 ga watan Agusta mai zuwa.

Masana shari’a da masu sharhi sun zargi Hukumar zabe da Jam’iyyun siyasa da gazawa wajen tantace ‘yan takarar zabe, abinda ya kai ga soke zaben Jihar Bayelsa da aka yi a wannan wata saboda gabatar da takardun bogi da ‘dan takarar mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa a karkashin Jam’iyyar APC yayi, abin da ya sa aka baiwa Jam’iyyar PDP kujerar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.