Isa ga babban shafi
Najeriya

Hannan Buhari ta nesanta kan ta da kama Anthony Okolie

‘Yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wato Hanan Buhari ta nesanta kan ta da kamun da jami’an hukumar tsaron DSS suka yiwa wani mutum mai suna Anthony Okolie suka kuma tsare shi na makwanni 10 saboda zargin amfani da layin wayar ta.

Hanan Buhari, 'yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Hanan Buhari, 'yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase
Talla

Lauyan Hanan, wato H.E. Shariff ya shaidawa kotu cewar layin wayar da ake magana akan sa, lallai na ta ne da tayi amfani da shi a baya, amma kuma ko da sunan wasa bata da masaniyar cewar jami’an DSS sun kama wanda ake zargin.

Hanan ta ce bata taba korafi ko kai kara cewar wani na amfani da layin ta ba ga jami’an tsaron DSS ko wata hukuma ta tsaro, saboda haka zargin cewar ta sa an kama Anthony kuma an ci zarafin sa ba daidai bane.

Anthony ya maka Hanan Buhari a gaban kotu ne inda yake tuhumar ta tare da hukumar DSS da kamfanin MTN a kotun Asaba cewar an ci zarafin shi wajen kama shi da kuma tsare shi na makwanni 10 saboda layin da ya saya daga hannun MTN.

Lauyan Anthony ya bukaci wadanda ake zargin su biya shi diyyar naira miliyan 500 a matsayin illar da suka masa wajen bata suna da kuma cin zarafi.

Rahotanni sun ce bayan tsare Anthony na makwanni 10 DSS sun sake shi bayan sun tirsasa shi ya sanya hannu kan wata takardar cewar ba zai shigar da su kara ba.

Kotun dake sauraron karar ta dage shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Maris mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.