Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan majalisar dokoki: ‘Yan Najeriya na ganin albashinku ya yi yawa – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa ‘yan majalisar dokokin kasar cewa ba su da kima a idon yawancin al’ummar kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Shugaban ya ce ‘yan Najeriya na kallon ‘yan majalisar a matsayin wadanda suke karbar albashi fiye da kima, alhali kuwa aikinsu kalilan ne.

Yana jawabi ne yayin bikin kaddamar da mujallar majalisar wakilan kasar ‘Green Chamber’.

Buhari wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed ya ce bijiro da mujalla mallakin majalisar zai canza irin kallon da al’umma ke wa majalisar dokokin.

Ya ce a ganin wasu ‘yan Najeriya, majalisar dokoki wuri ne da wasu ke zaune suna samun makudan kudade kan dan aikin da bai taka kara ya karya ba.

Ya ci gaba da cewa rashin sanin dimbim aikin da ‘yan majalisar ke yi ne ya sa wasu ke yi musu irin wannan kallo na hadarin kaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.