Isa ga babban shafi
Libya-Haftar

Gwamnatin Libya ta janye daga taron Geneva bayan hare-haren Haftar

Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan kasashen Duniya ta sanar da jingine halartan taron sulhu na Geneva da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya da zimmar ganin an tsagaita wuta a yakin da ke kokarin dawowa kasar.

Babban kwamandan Sojin Libya Khalifa Haftar tare da Firaministan kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.
Babban kwamandan Sojin Libya Khalifa Haftar tare da Firaministan kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Fethi Belaid, Khalil Mazraawi/AFP
Talla

Matakin Janyewar da Gwamnatin ta Firaminista Fayez al Sarraj daga taron na zuwa ne bayan sabbin hare-hare rokoki da Soji masu biyayya babban kwamandan Sojin kasar mai rike da galibin yankunan gabashi Khalifa Haftar suka kaddamar a birnin Tripoli a ci gaba da kokarinsu na ganin sun kwace iko da birnin tare da hambarar da gwamnati.

Wata sanarwa Gwamnatin Libyan na ce sun jingine halartan tattaunawar har sai an dauki matakin daya dace game da saba yarjejeniyar da aka kulla da bangaren Khalifa Haftar.

Sanarwar na cewa ba tare da tsagaita wuta ba duk wata tattaunawar sulhu ba zata yiwu ba, ana ta kai hare-haren bama-bamai a Tripoli.

Hare-haren na daga cikin yarjeniyoyin da aka karya a zaman sulhu da Rasha ta shirya, wadda take goyon bayan Khalifa Haftar, da kuma bangaren Gwamnatn hadin kan da ke samun goyon bayan kasar Turkiya.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya hare-haren Libya na baya-bayan nan ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 1, da sa wasu Karin mutane dubu 140 barin gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.