Isa ga babban shafi
Corona-Masar

An samu mutum na farko da ya kamu da coronavirus a Masar

Hukumomin kasar Masar sun sanar da samun wada ya kamu da coronavirus ko kuma COVID-19 a karon farko a nahiyar Afirka, cutar da yanzu haka ta kashe mutane kusan 1,400 a China.

Likitocin da ke kula da masu fama da cutar corona.
Likitocin da ke kula da masu fama da cutar corona. China Daily via REUTERS
Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar wadda ta tabbatar da samun wanda ya kamu da cutar, ta ce mutumin ba dan kasar Masar ba ne, kuma tana daukar matakan da suka dace wajen kula da shi.

Khaled Megahed, mai Magana da yawun ma’aikatar lafiyar ya ce tuni suka sanar da Hukumar lafiya ta Duniya WHO, yayin da aka killace mutumin a asibitin da ake kula da shi.

Masar ta kwashe 'Yan kasar ta 301 daga Wuhan a kasar China, daya daga cikin garuruwan da ke fuskantar bala’in wannan annoba, yayin da yanzu haka su ke killace a inda ake tsare da su na kwanaki 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.