Isa ga babban shafi
Afrika

An soma bukin addu'o'i ga marigayi Daniel Arab Moi

Tsohon Shugaban kasar Kenya Daniel Arap Moi wanda ya jagorancin kasar tsakanin shekarar 1978 zuwa 2002  da ya rasu ranar talata 4 ga watan Fabrairu yana da shekaru 95 a Duniya.Shugaban kasar Uhuru Kenyatta ne ya sanar da mutuwar tsohon shugaban wanda ya kwashe shekaru 24 yana mulkin Kenya, inda ya sanar da zaman makoki har zuwa lokacin da za’a yiwa Moi jana’iza, jana'iza da aka soma a yau litinin.

Marigayi tsohon Shugaban kasar  Kenya Daniel Arab Moi
Marigayi tsohon Shugaban kasar Kenya Daniel Arab Moi Reuters/George Mulala
Talla

Duban yan kasar ne yanzu haka suka soma halara a wurin da aka ajiye gawar tsohon Shugaban kasar da nufin yi masa bankwana, yayinda wasu daga cikin yan kasar ke zargin marigayin da mulkin kama karya lokacin da ya jagoranci kasar, duk da haka wasu na yaba masa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar a daidai lokacin da kasashen irin su Rwanda da Burundi da Somalia ke fama da yakin basasa.

Wani abinda ya mamaye lokacin mulkin sa shine bacewar Dala biliyan guda daga babban bankin kasar wajen fitar da gwal da lu’u lu’u na bogi zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.