Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Condo

Rikici ya hallaka mutane 200 cikin wata guda a Jamhuriyar Congo

Rahotanni daga Jamhuriyar dimokiradiyar Congo sun ce mutane kusan 200 aka kashe a tashe tashen hankula da ke cigaba da gudana a kasar, adadi mafi yawa tun bayan irin sa da aka samu a watan Yunin shekarar 2017.

Tawagar shugaban Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Felix Tshisekedi a ziyararsa yankin da rikicin kasar ya tsananta.
Tawagar shugaban Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Felix Tshisekedi a ziyararsa yankin da rikicin kasar ya tsananta. Charlotte Cosset/RFI
Talla

Kungiyar masu binciken Congo da ke da cibiya a New York da Human Rights Watch sun ce kungiyoyin 'yan bindiga tare da jami’an tsaro sun kashe akalla fararen hula 197 a cikin kwanaki 31 na shekarar da ta gabata.

Sanarwar ta ce akasarin wadanda aka kashe sun fito ne daga yankin Beni, kuma ana zargin 'yan tawayen ADF ne suka hallaka su.

Ko a watan jiya Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda rikicin kasar ta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke ci gaba da salwantar da rayukan jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.