Isa ga babban shafi
Mali-MDD

Hare-haren ta'addanci a Mali na illa ga kananan yara- MDD

Majalisar  Dinkin Duniya ta ce hare-haren ta'addanci da rikicin da ke cigaba da faruwa a Yankin Sahel na matukar illa ga daruruwan kananan yara, wajen kashe su baya ga jikkata wasunsu da kuma tilasta su rabuwa da iyayensu.

Wasu Soji da ke yaki da ta'addanci a Mali.
Wasu Soji da ke yaki da ta'addanci a Mali. AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Majalisar ta ce a shekarar bara, yara 277 aka kashe ko jikkatawa a kasar Mali, kamar yadda rahotan UNICEF ya bayyana, adadin da ya ribanya na shekarar 2018.

Rahotan ya ce yanzu haka daukacin kasashen da ke Yankin Sahel na fama da rikice rikice wadanda ke illa ga kanana yaran a matakai daban daban, yayin da ya tilastawa sama da miliyan guda da dubu 200 tserewa daga gidajen su.

Hare-hare kan fararen hula baya ga tashin bama-baman gefen hanya na ci gaba da ta'azzara a kasar ta Mali, matakin da ke haddasara asarar dimbin rayuka, duk kuwa da ikirarin gwamnatin kasar na daukar matakan yaki da kungiyoyin ta'addanci masu ikirarin jihadi.

Haka zalika cikin kasar ta Mali akwai tarin dakarun Sojin hadaka har da na Faransa da ke ikirarin yaki da ta'addancin, sai dai kawo yanzu masana na ganin rikicin kasar na ci gaba da ta'azzara ne sabanin lafawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.