Isa ga babban shafi
Amnesty-Gambia

Amnesty na zargin Gambia da kame 'yan jaridu

Kungiyar Amnesty International ta zargin gwamnatin Gambia da kama-karya wajen kama 'yan Jaridu ta na tsarewa baya ga kulle wasu tashohin labarai na Radio guda biyu, saboda zarginsu da kalubalantar salon kamun ludayin gwamnatin kasar.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Adama Barrow a Gambia.
Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Adama Barrow a Gambia. ROMAIN CHANSON / AFP
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar ya bayyana sa’oi 24 da suka gabata a matsayin mafi muni a Gambia tun bayan karbar mulkin Adama Barrow, sakamakon kama mutane 137 da suka shiga zanga zanga wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 3.

Gwamnatin kasar ta kuma rufe tashoshin rediyo guda 2 da suka hada ad King FM da kuma Home Digital FM duk dai a kokarinta na dakile mutane daga ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnatin.

Sai dai kawo yanzu al'ummar ta Gambia na ci gaba da gangamin don kalublantar gwamnatin ta Adama Barrow da suka bayyana da kasasshiya.

Mako na biyu kenan aka shiga al'ummar kasar na zanga-zangar adawa da gwamnati tare da neman dawowar tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh da ke gudun hijira.

Zanga-zangar dai ta biyo bayan yadda Barrow ya gaza cika alkawarin da ya dauka na sauka daga mulki bayan shekaru 3. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.