Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 27/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 27/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 27/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 27/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Gwamnati ta cimma matsaya da gwamnoni kan Amotekun

media Taron Gwamnonin yammacn Najeriya RFI/Hausa

Gwamnatin Najeriya tace ta kulla yarjejeniya da gwamnonin jihohin yammacin kasar guda 6 kan yadda shirin su na kafa rundunar tsaron da aka yiwa lakabi da Amotekun zai yi aiki ba tare da saba dokokin kasar ba.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana haka, bayan wani taro da yayi da gwamnonin jihohin dake yankin tare da ministan shari’a Abubakar Malami da kuma Sufeto Janar na Yan Sanda Muhammadu Adamu.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Laolu Akande yace gwamnonin suka bukaci ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin, amma sai ya sanya mataimakin sa Osinbajo ya wakilce shi.

Akande yace an samu fahimtar juna tsakanin bangarorin dangane da kafa rundunar, yayin da suka amince su sanya ta a karkashin shirin gwamnatin tarayya na samar da tsaron al’umma da kuma yin dokokin da suka dace.

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da yayi Magana a madadin gwamnonin ya tabbatar da matsayin mataimakin shugaban kasar da kuma aniyar su na ganin an warware matsalar ta fannin siyasa da kuma dokar kasa.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure