Isa ga babban shafi
Gambia

Al'ummar Gambia na zanga-zangar bukatar dawowar Yahya Jammeh

Dubun-dubatar magoya bayan tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh a Banjul babban birnin kasar sun gudanar da wani gangamin bukatar dawowarsa daga gudun hijirar da ya ke tun bayan sauka daga mulki.

Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh.
Tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins/Files
Talla

Zanga-zangar wadda ta faro kwanaki kalilan bayan fitar wani faifan sautin tsohon shugaban na Gambia da ke bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasar bai haramta masa dawowa ba, hasalima karkashin tanadin kundin mulkin na Gambia dole gwamnati ta bashi cikakkiyar kariya da kulawa.

Yahya Jammeh wanda ya mulki Gambia tsawon shekaru 22, ya tsere daga kasar ne zuwa Equatorial Guinea bayan shan kaye a zaben 2017 hannun Adama Barrow da ke jagoranci kasar a yanzu.

Sai dai bukatar dawowar tsohon shugaban ta taso ne bayan takaddamar baya-bayan nan, da ta dabaibaye batun saukar shugaba Adama Barrow daga mulki, bayanda shugaban a nuna bukatar ci gaba da jan ragamar kasar zuwa cika shekaru 5 a mulki, batun da ya ci karo da ikirarinsa yayin yakin neman zabe da ya sha alwashin cewa ba zai cika shekaru 5 a mulkin kasar ba.

Alhamis din nan, dubun-dubatar magoya bayan hadakar jam’iyyar kawancen Jammeh ta APRC ne suka gudanar da kakkarfar zanga-zangar inda suka rika kiraye-kirayen bukatar dawowar tsohon shugaban kasar don cetonsu.

Ko a watan jiya sai da al’ummar Gambia suka gudanar da makamanciyar zanga-zangar suna neman lallai shugaba Barrow ya ajje mukaminsa, yayinda a yanzu haka suka sake shirya makamanciyar zanga-zangar don nuna adawa da shugaban tare da nuna goyon baya ga tsohon shugaban a ranakun 19 da 20 ga watan nan.

Daruruwan masu zanga-zangar sun bukaci kungiyar ECOWAS ta girmama sanarwarta ta wancan lokaci yayin hijirar Yahya Jammeh da ta nuna cewa yana da ‘yancjn dawowa kasar bayan shekaru 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.