Isa ga babban shafi
Nijar - Sahel

IS ce ta kai harin da ya kashe sojojin Nijar

Kungiyar IS reshen Afrika ta yamma "ISWAP" ta dauki alhakin mummunan harin da aka kaiwa sansanin sojin Jamhuriyar Nijar a Shinagodar dake Tillaberi, inda ta halaka dakarun kasar kusan 90, a ranar alhamis 9 ga watan Janairun 2020.

Wasu sojojin Nijar yayin gudanar da atasaye.
Wasu sojojin Nijar yayin gudanar da atasaye. US Army/Richard Bumgardner
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ISWAP ta yi ikirarin kashe sojojin Nijar 100.

Da fari dai gwamnatin Nijar ta ce dakarunta 25 ne suka kwanta dama yayin gumurzun da suma suka halaka akalla 77 daga cikin 'yan ta'adda, sai dai a karshen mako hukumomin na Nijar suka ce adadin sojin kasar da suka mutu ya karu zuwa 89.

Farmakin dai shi ne mafi muni Nijar ta fuskanta na rasa adadin dakarun kasar mai yawan gaske a rana guda.

An dai harin ta’addancin ne a yankin na Tillaberi, inda a watan disambar 2019, mayakan na ISWAP suka kashe sojojin Nijar 71 yayin gumurzun da suka yi.

Wata kididdiga a baya bayan nan da majalisar dinkin duniya ta fitar, ta nuna cewar hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa a baya bayan nan, a kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun salwantar da rayukan akalla mutane dubu 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.