Isa ga babban shafi
Libya-Rasha

Haftar ya fice daga zauren kulla yarjejeniyar zaman lafiyar Libya

Marchal Khalifa Haftar, babban kwamandan sojin da ke rike da mafi yawan yankunan gabashin kasar Libya, ya baro birnin Moscow na Rasha ba tare da sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita tsakanin bangarorin kasar 2 masu rigima da juna ba.

Khalifa Haftar, babban kwamandan Sojin Libya mai iko da manyan yankunan kasar.
Khalifa Haftar, babban kwamandan Sojin Libya mai iko da manyan yankunan kasar. Abdullah DOMA / AFP
Talla

Yayin taron da ke tattaunawa kan rikicin kasar ta Libya da Rasha ke karbar bakonci wanda ke samun halartar Turkiya mai mara baya ga gwamnatin Libyan da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, tuni Firaminista Fayez Al-sarraj ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar.

To sai dai tun kafin ya tashi zuwa birnin na Moscow, Firaministan al-Sarraj wanda ke yi wa al’ummar kasar Libya jawabi, ya ce a shirye ya ke a zauna lafiya a kasar amma bisa sharuddan dole ni Hafta ya janye daga yankuna da ya mamaya a baya-bayan nan.

Khalifa Haftar dai ya fice daga dakin taron inda ya yi watsu da bukatun da yarjejeniyar zaman lafiyar ta kunsa, Ko da dai Rashan wadda ke matsayin babbar kawa ga Haftar ta sha alwashin shawo kan matsalar.

A wani taron manema labarai da Lavrov kakakin Kremlin ya gabatar a Colombo, ya ce Rasha za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin Khalifa Haftar ya amince da yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.