Isa ga babban shafi
Mali-Sahel

Bom a gefen hanya ya hallaka Sojin Mali 5

Akalla Sojin Mali 5 aka tabbatar da mutuwarsu yau Litinin bayan da motarsu ta taka wata nakiya da ke gefen titi akan hanyarsu ta zuwa yankin Alatona da ke iyaka da Mauritania.

Wata motar Soji da Bom ya lalata.
Wata motar Soji da Bom ya lalata. REUTERS/Feisal Omar/File Photo
Talla

Majiyar tsaro a kasar ta Mali ta bayyana cewa bom din ya lalata 5 daga cikin jerin gwanon motocin Sojin da ke tafiya.

Mai magana da yawun gwamnatin Mali Yaya Sangare ya bayyana cewa tuni aka aike da karin wasu dakarun don fatattakar ‘yan ta’addan da ke yankin.

Harin na yau dai kari ne kan hare-haren baya-bayan nan da ya hallaka Sojin kasar ta Mali fiye da 140 daga watan Satumba zuwa Disamban da ya gabata.

Duk da tarin Sojin Faransa dubu 4 da dari 5 da ke jibge a Malin da kuma karin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu 13 da ke kasar har yanzu hare-haren ta’addanci na ci gaba da tsananta a kasar yayinda daruruwan sojoji da fararen hula ke ci gaba da rasa rayukansu.

Tun daga shekarar 2012 ne Mali ta fara fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.