Isa ga babban shafi
Liberia

Al'ummar Liberia sun gudanar da zanga-zangar kyamar gwamnati

Dubun-dubatar al’ummar Liberia sun gudanar da wata gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati yau Litinin da nufin kalubalantar matakan da shugaba George Weah ke dauka kan tattalin arzikin kasar da ke ci gaba da fuskantar koma baya.

Al'ummar Liberia yayin zanga-zangar kyamar gwamnati.
Al'ummar Liberia yayin zanga-zangar kyamar gwamnati. CARIELLE DOE / AFP
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa fiye da mutum dubu 3 ne daga sassan kasar suka taru a Manrovia babban birnin kasar don gudanar da zanga-zangar tun da sanyin safiyar yau Litinin duk da dai jami’an tsaro sun yi barazanar hana jama’a dandazo a muhimman wurare.

Zanga-zangar dai itace irinta ta 3 da George Weah ke fuskanta bayan karbar ragamar shugabancin kasar ta yammacin Afrika wadda yanzu haka ke cikin mawuyacin hali sanadiyyar tabarbarewar tattalin arziki, tsadar rayuwa da kuma karuwar marasa aikin yi.

A makon da ya gabata ne al’umura suka tsananta bayan da gwamnati ta haramta zanga-zangar tare da haramtawa jami’an tsaro baiwa masu zanga-zangar kariya bisa kare matakin ta da cewa zanga-zangar wadda bangaren adawa suka shirya gudanarwa tazo dai dai da lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da hasashen iya fuskantar rikici a zanga-zangar da ya tilasta kulle shagunan kasuwanci, an gudanar da zanga-zangar cikin lumana, inda masu zanga-zangar rike da alluna dauke da rubutun neman gwamnati ta dauki mataki kan tattalin arzikin kasar suka rika ife-ife da rera wakokin neman sauyi tare da kalubalantar kokarin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.