Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Harin bam ya halaka yara dalibai a Burkina Faso

Akalla fararen hula 14, mafi akasarinsu kananan yara dalibai ne suka halaka yau asabar a Burkina Faso, bayan tarwatsewar wani bam da aka binne a gefen hanya.

Wasu sojojin Faransa yayi binciken bama-baman da ake binnewa a gefen hanya a arewacin Burkina Faso.
Wasu sojojin Faransa yayi binciken bama-baman da ake binnewa a gefen hanya a arewacin Burkina Faso. AFP/Michele Cattani
Talla

Mummunan lamarin ya auku yayinda motar daliban ta taka bam din lardin Souro a yankin arewa maso yammacin kasar mai iyaka da kasar Mali.

Zuwa yanzu mutane hudu aka tabbatar da sun jikkata a harin, bayaga 14 da suka halaka.

A wani labarin kuma, rundunar sojin ta Burkina Faso ta ce mahara sun farwa Jandarmomi a yankin areawcin kasar, inda aka gwabza fadan da suka yi nasarar halaka ‘yan ta’adda da dama.

Wata kididdigar majalisar dinkin duniya, ta nuna cewar tun bayan soma kai hare-haren ta’addanci a Burkina Faso cikin shekarar 2015, sama da mutane 750 suka halaka, yayindawasu akalla dubu 560 suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.