Isa ga babban shafi
Chadi - Najeriya

Chadi ta janye dakarunta dake yakar Boko Haram a Najeriya

Rundunar sojin Chadi ta sanar da janye dakarunta daga Najeriya, da suke shafe shekaru suna tallafawa takwarorinsu na kasar wajen yakar kungiyar Boko Haram.

Wasu sojojin kasar Chadi, bayan fatattakar mayakan Boko Haram daga garin Damasak a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. 18/3/2015.
Wasu sojojin kasar Chadi, bayan fatattakar mayakan Boko Haram daga garin Damasak a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. 18/3/2015. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

A yau asabar ne dai 4 ga Janairun 2020, kakakin rundunar sojin Chadi Kanal Azem Bermandoa ya bayyana daukar matakin yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kanal Azem ya ce a Juma’ar da ta gabata Chadi ta janye baki dayan dakarunta dubu 1 da 200 dake taimakawa Najeriya wajen yakar Boko Haram, bayan da suka kammala aikinsu.

Sai dai Babban Hafsan sojin kasar ta Chadi Janar Tahir Erda Tahiro, ya ce muddin kasashen dake fama da rikicin Boko Haram za su ci gaba da kawance, akwai yiwuwar sake tura wasu dakarun na Chadi zuwa Najeriya, domin ci gaba da aikin samar da tsaro.

Matakin kasar Chadi ya zo ne a dai dai lokacin da wasu shugabannin yankin arewa maso gabashin Najeriya suka bukaci dakatar da shirin gwamnatin kasar na janye dakarun sojojinta daga wasu sassan Najeriya domin maye gurbinsu da 'Yan Sanda da kuma jami'an tsaro na Civil Defence.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.