Isa ga babban shafi
Afrika

Shugabannin Afrika sun aike da sakonnin sabuwar shekara

Shugabannin Afirka da dama ne suka fitar da sakonni ga al’ummominsu dangane da shiga sabuwar shekara ta 2020, shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da na Nijar Issoufou Mahamadou, sun mayar da hankali ne a game da tsanantar ta’addanci a kasashensu, yayin da takwaransu na kasar Chadi ya nuna bacin ransa kan yadda kasashen Duniya suka ki bayar da tallafin da ya dace don shawo kan matsalar.

Wasu daga cikin Shugabanin Afrika
Wasu daga cikin Shugabanin Afrika CNN.com
Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kuwa, ya ce akwai kyakkyawan fata ga makomar kasar a dai-dai lokacin da aka shiga sabuwar shekarar, sannan ya jaddada aniyarsa ta samar wa kasar ingataccen tsarin gudanar da zabe a cikin shekaru uku masu zuwa.

Shugaban Guinea Conakry Alpha Conde, a nasa sakon ya jaddada aniyarsa ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara ne, yayin da takwaransa na Senegal Macky Sall ya bayyana farin cikinsa a game da yiyuwar fara amfani da sabbin kudaden Eco a wasu kasashen yammacin Afrika a shekarar bana ta 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.