Isa ga babban shafi
Afrika

Ana tsare da wani dan jarida a Morocco

A kasar Morocco dubban mutane ne suka banzama saman tittunan birnin Rabat don nuna bacin ran su biyo bayan kama wani dan jarida Omar Radi dake tsare yanzu haka bisa laifin bayyana ra’ayin sa da yayi dangane da wani mataki da kotu ta dau a watan Afrilu.

Wasu daga cikin kungiyoyi dake kare hakokin yan jarida a Morocco
Wasu daga cikin kungiyoyi dake kare hakokin yan jarida a Morocco STRINGER / AFP
Talla

Dan jaridar mai shekaru 33, ana zargin sa da ya yadda labaren da kan iya haifar da yammuci biyo bayan hukunci daga kotu dangane da shara’ar wasu mutanen wata kungiya mai suna Hirak, kungiyar dake adawa da yada hukumomin Morocco ke tafiyar da siyasa a arewaci kasar.

Dan jaridar Omar Radi da ya rubuta batanci zuwa alkalan kotu zai iya fuskantar dauri na shekara daya a kurkuku, matakin da kungiyar kare hakokin bil Adam Human rigths Watch ta yi Allah wadai da shi.

Kasar Morocco na daga cikin jerry kasashe da manema labarai ke fuskanatar matsalloli wajen tafiyar da ayyukan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.