Isa ga babban shafi
Somalia

Harin ta'addanci ya halaka mutane da dama a Mogadishu

Jami’an tsaron Somalia sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 76, da kuma jikkata wasu kimanin 90, biyo bayan fashewar bam din da aka danawa wata mota a yankin da ake samun cinkosson jama’a da ababen hawa.

Jami'an tsaron kasar Somalia a shingen binciken ababen hawa da aka kai harin bam a birnin Mogadishu. 28/12/2019.
Jami'an tsaron kasar Somalia a shingen binciken ababen hawa da aka kai harin bam a birnin Mogadishu. 28/12/2019. REUTERS/Feisal Omar
Talla

An dai kai mummunan harin ne a gaf da wani shingen binciken ababen hawa, da kuma babban ofishin tattara haraji a birnin na Mogadishu

‘Yan sanda sun ce mafi akasarin wadanda suka halaka a harin daliban Jami’a ne, sai kuma wasu ‘yan kasar Turkiya 2.

Harin bam din na yau dai shi ne mafi muni da aka kai a birnin Mogadishu cikin shekaru 2.

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.