Isa ga babban shafi
Najeriya

El-Rufai ne kawai zai iya sakin El - zakzaky

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce gwamnatin jihar Kaduna ce kawai za ta iya yanke shawarar sakin shugaban mabiya akidar Shi’a a kasar, Sheikh Ibrahim El – Zakzaky.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban 'yan Shi'a a Najeriya.
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban 'yan Shi'a a Najeriya. YouTube
Talla

Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami, wanda ya bayyana haka ya ce a karkashin dokokin jihar Kaduna ne ake wa fitaccen Malamin shari’a.

Ya ce laifukan da malamin ya aikata sun sha bambam da wadanda Omoyele Sowore da Sambo Dasuki suka aikata.

Tun da ministan shari’ar Najeriya ya bada umurnin sakin Dasuki da Sowore mutane suka shiga neman bayani kan makomar El- Zakzaky daga gwamnatin Tarayyaar Najeriya.

Su ma mabiya El- Zakzaky sun zafafa fafutukar neman a saki malamin nasu tun bayan da aka saki Dasuki da Sowore a ranar jajibirin Kiristimeti.

An kama El-Zakzaky da maidakinsa Zeenat ne a shekarar 2015 a Kaduna, bayan sa in sa tsakanin ‘yan Shi’a da ayarin babban hafsan sojin Najeriy, Laftnar Janar Tukur Yusuf Buratai, lamarin da yayi sanadin mutuwar ‘yan Shi’a da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.