Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Kungiyoyin fararen hula 183 sun nesanta kansu da ikirarin Ganduje

Akalla kungiyoyin fararen hula 183 a jihar kano da ke arewacin Najeriya ne suka nesanta kansu da ikirarin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da ke bayyana cewa wasu daga cikinsu ne suka aike masa da takaddamar bukatar tube Mai martaba sarki Muhammadu Sanusi na II.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. vanguard
Talla

Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa Abba Anwar ya fitar ta ce ya karbi takardu daga hadakar kungiyoyin fararen hula 35 da bai bayyana sunansu ba, wadanda ya ce sun bukaci gwamnan ya tube Mai martaba sarki Sanusi na II.

Cikin sanarwar Gwamnan ya ce, kungiyoyin 35 sun zargi Mai martaba Sarki Sanusi da kin biyayya ga gwamnati mai ci karkashin Abdullahi Ganduje na Jam’iyyar APC.

Sanarwar ta bayyana sunan wani Comrade Ibrahim Ali a matsayin wanda ya jagoranci hadakar kungiyoyin na fararen hula 35 wadanda ko guda daya ba a fayyace sunanta a cikin sanarwar ba.

Sai dai sanarwar da halastacciyar hadakar kungiyoyin fararen hula a jihar ta Kano ta KCSF ta fitar a yau Juma’a, ta nesanta kanta da bukatar tsige Mai martabar ta bakin kakakinta Ibrahim Wayya Rano.

Ka zalika cikin sanarwar ta KCSF, hadakar kungiyoyin ta bukaci gurfanar da Comrade Ibrahim Ali wanda ta ke zargi da yi mata sojan gona wajen aikewa da sakon wasikar ba tare da masaniyarta ba.

Baya ga sanarwar ta daban, kungiyar dai ta kuma aike da wata budaddiyar wasika ga Gwamna Ganduje tare da nesanta kanta da waccan wasika ta farko.

Ana dai ci gaba da fuskantar dambarwar siyasa ne tsakanin Mai martaba sarkin na Kano da Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan jihar mai ci tun bayan zaben shekarar nan da gwamnatin Kanon ta zargi Sarkin da mara baya ga Jam’iyyar adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.