Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan ta'adda sun kashe jami'an agaji 4 da suka yi garkuwa da su a Najeriya

Kungiyar ACF mai rajin yaki da yunwa a kasashen da rikici ya daidaita ta tabbatar da kisan jami’anta cikin wasu mutane 4 da mayakan kungiyar ta'addanci suka hallaka a Najeriya.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce mutanen 4 dukkaninsu ‘yan Najeriya na cikin mutane 6 da kungiyar ta yi garkuwa da su tun cikin watan Yulin da ya gabata.

Kungiyar ta ACF ta ce tun a ranar 18 ga watan Yuli ne kungiyar ta yi garkuwa da mutanen inda tun a watan Satumba suka hallaka guda.

A cewar kungiyar ta ACF da babbar shalkwatarta ke Faransa, cikin mutanen da aka kashe har da direbobinsu dukkanninsu ‘yan Najeriya.

Kungiyar dai ba ta kira sunan Boko Haram ko ISWAP a matsayin wadda ta aika kisan, ta dai bayyana makasan a matsayin 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.