Isa ga babban shafi
Afrika

Taron kawo karshen rashin tsaro a Mali

A gobe Asabar za a fara wata tattaunawa don lalubo mafita game da rikicin Mali da ya ki ci ya ki cinyewa. Yan kasar ta Mali na cigaba da bayyana damuwa matuka ganin rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassan kasar.

Dakarun yaki da ta'addanci na  Faransa a yankin Sahel
Dakarun yaki da ta'addanci na Faransa a yankin Sahel Daphné BENOIT / AFP
Talla

Tattaunawar da zata kunshi bangarori dabam – dabam, zata baiwa shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita kwarin gwiwa bayan tsawon lokaci na rikicin mujahidai da na kabilanci da ya kawo cikasa ga kasar sa Mali.

Sojojin Malin 140 suka mutu tun a watan Satumba, a rikicin da ya bazu a ilahirin yankin Sahel, inda cikin wannan makon sojojin Nijar 71 suka gamu da ajalinsu a harin da IS ta dau alhaki, lamarin da ya kai Shugaban kasar Burkina Faso bayyana matsayin sa da kuma kira zuwa kasashen dake dafawa yankin Sahel don ganin sun taka gaggarumar rawa wajen kawar da mayakan jihadi a yanking a baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.