Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 17/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano
Afrika

'Yan ta'adda sun kashe mutane a otel din Somalia

media Wasu daga cikin mayakan al-shebaab REUTERS/Feisal Omar

Akalla mutane biyar sun rasa rayukansu a wani harin da mayakan jihadi suka kaddamar kan wani otel da ke babban birnin Mogadishu na Somalia kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka tabbatar , yayin da rahotanni ke cewa, an yi nasarar hallaka daukacin maharan bayan dauki-ba-dadin da aka yi da su na tsawon sa’o’i.

Kungiyar al-Shebab ta dauki alhakin harin wanda aka kai kan ote din SYL wanda fitattun ‘yan siyasa da manyan sojoji da jami’an diflomasiya ke yawan zama a ciki.

Sanarwar da rundunar ‘yan sanda ta fitar, ta ce, jami’anta sun kawo karshen tashin hankalin, inda  kuma suka kubutar da mutane sama da 80 da suka hada da jami’an gwamnati.

Jami’an tsaro biyu da fararen hula uku sun rasa rayukansu a harin na ta’addanci , yayin da sojoji biyu da fararen hula tara suka jikkata.

Shaidu sun rawaito cewa, maharan sun yi shigar burtu, inda suka sanya kakin ‘yan sanda, abin da ya ba su damar kusantar otel din cikin sauki tare da bude wuta kan mai uwa da wabi.

Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure