Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 27/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 27/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 27/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 27/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Mutane miliyan 9 na fuskantar tsananin yunwa a Afrika -Rahoto

media Najeriya ce kan gaba da yawan mayunwata miliyan 4 kana Nijar da miliyan 1 da rabi tukuna BurkinaFaso da adadin mutum miliyan 1 da dubu dari 2. RFI/Laura Angela Bagnetto

Wani rahoton masana kan kamfar abincin da nahiyar Afrika ke fuskanta ya nuna cewa, kimanin mutane miliyan 9 da dubu dari 4 na tsananin bukatar agajin abinci a kasashen nahiyar musamman na yankin Sahel.

Cikin rahoton na masana da wata kungiya mai rajin tabbatar da wadatuwar abinci ta duniya tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya suka fitar a yau litinin, ya bayyana cewa kasashen Najeriya Nijar da kuma Burkina Faso su ne kan gaba wajen shiga halin tsaka mai wuya sanadiyyar yunwar.

Rahoton kungiyar mai zaman kanta ya bayyana cewa binciken da suka gudanar tsakankanin watan Oktoba zuwa Disamban da muke ciki, akwai mutane miliyan 9 da dubu dari 4 wadanda ke halin tsaka mau wuya kuma su ke tsananin bukatar agajin abinci.

Cikin adadin na fiye da miliyan 9 rahoton kungiyar ya nuna adadin mutane miliyan hudu da ke tsananin bukatar agajin abinci na Najeriya, yayinda Jamhuriyar Nijar ke da adadin mutane miliyan 1 da dubu dari 5 kana Burkina Faso da adadin mutum miliyan 1 da dubu dari 2.

Cikin rahoton kungiyar wadda ta fitar a yau Litinin yayin babban taronta na shekara-shekara a Faransa ta ce matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, akwai yiwuwar adadin mutanen da za su bukaci agajin abinci daga watan Yuni zuwa Agustan shekarar 2020 ya kai miliyan 14 da dubu dari 4 a nahiyar ta Afrika.

Rahoton kungiyar ya alakanta matsalar kamfar abincin da rikicin da yak i ci yaki cinyewa a nahiyar, baya ga sauyin yanayi da kuma gazawar shugabannin kasashen.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure