Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 21/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 21/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

An gano gawar mutane 3 cikin 21 da Boko Haram ta sace a Kamaru

media Wasu dakarun sojin kasar Kamaru. Edwin Kindzeka Moki/AP/SIPA

A kasar Kamaru an gano gawarwakin mutane uku da ‘yan Boko Haram suka sace tun ranar Alhamis din da ta gabata a wani gari mai suna Tokomari da ke cikin gundumawar Kolafata kusa da iyakar kasar da Najeriya.

Bayanai sun ce daga cikin mutanen uku da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kashe har da mace daya, kuma dukanninsu an yi masu yanka rago ne.

Majiyoyin tsaron Kamaru da suka tabbatar da farmakin na ranar Alhamis sun bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun yi garkuwa da fararen hula akalla 21 gab da kan iyakar kasar da Najeriya mai fama da rikicin ta’addanci.

Majiyar tsaron ta tabbatar da cewa 4 cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun yi nasarar kubuta yayinda kawo yanzu ba a san halin da sauran mutanen ke ciki ba.

Cikin sauran mutanen da suka rage a hannun mayakan na Boko Haram a yanzu haka harda mata da kuma kananan yara.

 

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure