Isa ga babban shafi
Rwanda

An fara allurar rigakafin Ebola a Rwanda

Gwamnatin Rwanda ta kaddamar allurar rigakafin kariya daga cutar Ebola a yammacin kasar iyakar ta da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

Kan iyakar Rwanda da garin Goma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Kan iyakar Rwanda da garin Goma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo REUTERS/Djaffer Sabiti
Talla

A Lahadi nan ne aka kaddamar da wannan allura ta rigakafi karo na farko don kare al’ummar kasar da ke rayuwa a yankunan da ke kusa da iyaka da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, kasar da cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a wannan shekarar.

Akalla mutane dubu 200 ne ake fatan yi wa allurar rigakafin a lardunan Rubuvu da kuma Rasizi da ke gabar kudu da kuma arewacin kogin Kivu, da ke matsayin iyakar da ta raba wadannan kasashe biyu.

Wani kamfanin rarraba magunguna da ke kasar Belgium ne ya samar wa Rwanda wannan allura da kamfanin Johnson&Johnson ya sarrafa kamar dai yadda minista a ma’aikatar lafiyar kasar ta Rwanda Diane Gashumba ta sanar.

Duk da cewa ba a samu labarin bullar cutar ta Ebola a cikin kasar ta Rwanda ba, amma Hukumar Lafiya ta Duniya ta shawarci kasashen yankin musamman masu makotaka da Congo su tabbatar da cewa sun yi wa al’ummominsu wannan allura da za ta iya share tsawon watanni 12 tana aiki a jikin dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.