Isa ga babban shafi
Nijar-Boko Haram

An yaye tubabbun mayakan Boko Haram da suka koyi sana'o'i a Nijar

Hukumomin Jamhuriyar Nijar yau sun yaye mayakan boko haram 110 da aka horar da su a karkashin wani shirin sake tunanin su da kuma koya musu sana’oi a yankin Diffa, cikin su har da 'yan Najeriya 47.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

A bikin da aka yi a Goudoumari da ke da nisan kilomita 200 daga Diffa, an rantsar da tsoffin mayakan da Alkur’ani mai girma, kafin mika musu takardar shaidar kammala zama a cibiyar, tare da karbar kayan aiki dangane da sana’ar da suka koya.

Wani daga cikin wadanda aka horar Ari Mallam ya nemi gafarar iyalan sa da al’ummar Nijar da na Afirka kan yaudarar da ya ce Boko Haram ta yi musu na zuwa Jihadi, inda ya ce yanzu bukatar sa ita ce zaman lafiya da jama’a.

Ministan cikin gida Bazoum Mohammed ya ce ranar Litinin za’a baiwa wadannan mutane 110 damar tafiya kauyuka da garuruwan da suka fito.

Ita dai wannan cibiya da aka kafa a watan Disambar shekarar 2016, ya zuwa yanzu ta horar da mutane sama da 240 cikin su har da mata da yara, wadanda suka kwashe wata 6 suna samun horo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.