Isa ga babban shafi
Najeriya

IPOB ta dauki alhakin hari kan Ministan sufurin Najeriya

Kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra a Najeriya IPOB ta dauki nauyin farmakin da aka kaiwa Ministan sufurin kasar Rotimi Ameachi a kasar Spain jiya Juma’a.

Nnamdi Kanu shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra.
Nnamdi Kanu shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra. STRINGER / AFP
Talla

Cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa tsaginta da ke Spain ya karbi umarnin kai farmakin daga jagoranta Nnamdi Kanu, kuma za su ci gaba da farmakar duk wani shugaban Najeriya a duk inda suka samu dama.

A jiya Juma’a ne dai Ministan sufurin na Najeriya Rotimi Amaechi ya sanar da aukuwar lamarin a shafinsa na Twitter ya ce, jami’an ‘yan sandan Spain sun fatattaki maharan kafin yi masa lahani.

Ko a 'yan kwanakin baya, sai dai aka kai makamancin wannan harin kan Sanata Ike Ekweremadu a daidai lokacin da yake halartar taro a kasar Jamus, yayin dakungiyar IPOB ta dauki alhakin harin a wancan lokaci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.