A wasanni 54 da ya buga a wannan shekarar Messi ya ci kwallaye 46 kana ya taimaka aka ci 17; a cikin kwallayen, 41 a Barcelona ya ciyo su, nan ne kuma ya taimaka aka ci kwallaye 15.
A lokacin da yake jawabi zuwa manema labarai Lionne Messi ya bayyana cewa ba shida lokacin da zai tsaya domin shawar wannan kayauta da aka ba shi ,dalili,lokaci na tafiya, a duk lokacin da ya tsaya ya waiwaya baya ya kan hango cewa ba shida nisa da ritaya daga fagen tamola,duk da yake da sauran shekaru a gaban sa .
Messi ya jaddada cewa lokaci ne na godiya ta musaman zuwa abokanin tafiya dama kungiyar sa ta Barca ,nasarorin da ya samu ,nasarorin kungiyar sa ce.
Lionnel Messi mai shekaru 32 ya tashi ga baki daya da ballon d’or guda shida a tarihin sa, 2009, 2010, 2011, 2012, 2015 sai 2019.
Cristianno Ronaldo na da Ballon D’or biyar,yayinda idan muka duba rubu mu za mu iya zana Johan Cruff,Michel Platini,Marco Van Basten dukan su da ballon d’or uku-uku.
A Karshe Messi ya bayyana cewa a duk lokacin da ya je ritaya daga buga kwallo to fa , a wannan lokaci ne zai yi tsayawa domin duba irin nasarori da ya samu da kyaututuka.
Bangaren masu tsaron raga, Alisson Becker dan kasar Brazilmai tsaron ragar Liverpool a Ingila ne ya lashe kyautar ballon d’or da aka yiwa sunan kyautar Yachine.
Bangaren mata Rapinoe mai shekaru 34 ce ta lashe wannan kyauta ta ballon d’or,kar mu manta da cewa a watan Satumba da ya gabata ta kasance yar wasa da aka bayyana a matsayin wace ta yi fice a shekara ta 2019 daga hukumar Fifa.