Isa ga babban shafi
Wasanni

A yau za a bayar da ballon d'Or a Paris

A yau litini za a bayar da kyautar ballon d’or da wata mujalla a Faransa da aka sani da France Football ta shirya a birnin Paris.Tsohon dan kwallon kafar Cote D’Ivoire Didier Drogba ne shugaban taron da zai gudana a wani gidan kalo mai suna Theatre du Chalet.A wannan bikin da zai hada masu ruwa da tsaki a Duniyar kwallon kafa ,masu zabe ko kuma tattance dan wasan da ya dace ya lashe wannan kyauta sun hada da kwarraru a fani jarida 180 .

Kyautar Ballon D'Or
Kyautar Ballon D'Or AFP
Talla

A jerry yan wasa da aka fitar da sunayen su da nufin za su iya lashe wannan kyauta za mu iya zana daga Nahiyar Afrika Sadio Mane dake taka leda a Liverpool, Pierre Emerik Aubameyang daga Gabon dake kuma taka tamola a Arsenal.

Hasashen manazarta ya koma zuwa dan wasan Barca Lionnel Messi duk da yake akwai yan wasa da ba a fida tsamanin za su iya kasancewa sahun gaba, Cristiano Ronaldo dake taka leda a Juventus, Karim Benzema,Virgil Van Dijk a Liverpool, Hugo Lioris, Sergio Aguero Manchesterd city, kadan daga cikin sunayen yan wasa bangaren maza daka fitar dake jerry masu neman wannan kyauta.

Bangaren mata ,za mu iya zana Saam Kerr yar Austria dake taka leda a Chicago Red Stars, Ellen White mnachesterd City, Lucy Bronze a Lyon, Sarra Bouhadi a Lyon, Wendie Renard a Lyon, Lieke Martens a Barca, da Megan Rapinoe yar Amurika dake taka leda a Reign.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.