Isa ga babban shafi
Namibia

Shugaba Geingob na Namibia ya sake lashe zaben kasar

Shugaban Kasar Namibia Hage Geingob ya yi nasarar lashe kujerar shugabancin kasar a wa’adi na biyu da rinjayen kashi 56.3, rinjayen da ke matsayin mafi karanci da wani shugaba akan kujerar mulki ya samu a kasar cikin shekaru 30. 

Shugaban kasar Namibia Hage Geingob
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob
Talla

Zaben wanda aka fafata tsakanin 'yan takara 11 shi ne irinsa na farko da al'ummar kasar suka yi yunkurin juya baya ga Jam'iyyar SWAPO wadda ke mulkin kasar tsawon shekaru 30 tun bayan samun 'yancin kai daga Afrika ta kudu a shekarar 1990.

Ka zalika wannan ne karon farko da Jam'iyyar ke samun rinjayen kasa da kashi 60 sabanin kashi 87 ko fiye da ta saba samu a ilahirin zaben da ya gudana.

Akwai dai zarge-zargen rashawa, kama karya da kuma nuna wariya baya ga rashin aikinyi da tabarbarewar tattalin arziki da ta dabaibaye wa'adin farko na gwamnatin shugaba Geingob wadda ake ganin ta haddasawa jam'iyyar koma baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.