Najeriya za ta fara ginin bututun gas daga kudu zuwa Arewa
Gwamnatin Najeriya na gab da fara aiki ginin bututun iskar gas da zai rika dakon gas daga kudanci zuwa arewaci a wani mataki na saukaka harkar safarar sinadarin baya ga fadada ayyukanta a sassan kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sanarwar da mai Magana da yawun shugaban Najeriyar Malama Garba Shehu ya fitar ta nuna cewa Nututun iskar gas din zai taso daga Ajaokuta zuwa Kaduna kana ya isa Kano don saukakawa al’umma.
Sanarwar ta Garba Shehu ta ruwaito shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari yayin jawabinsa a taron kasashe masu fitar da iskar gas karo na 5 da ke gudana a Malabo na Equatorial Guinea na cewa suna kan hanyar fadada hanyoyin safarar iskar gas a cikin Najeriya gabanin dasa bututun da zai basu damar isar ga iskar ta gas ga sauran kasashen Nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu