Ana ci gaba da zanga-zanga a Algeria
Masu bore a Algeria sun gudanar da gaggarumar zanga-zanga a ranar juma’a a babban birnin kasar Aljas don nuna rashin amincewar su da ka’aidojin da hukumar zabe da gwamnatin rikon kwariya suka gindaya dangane da zaben Shugaban kasar da suka rage makwani biyu a yi.
Wallafawa ranar:
Tun bayan saukar Abdel Aziz Bouteflika tsohon Shugaban kasar,masu bore a kasar na zargin gwamnatin rikon kwariya da gudanar da salon siyasa mai kama da gwamnatin Abdel Aziz Bouteflika.
Masu zanga-zangar dauke da aluna sun bayyana cewa babu ta yada za aje wannan zabe mudin hukumomin dake nan ba su bi umurni jama’ar kasar ba.
Akalla mutane 25 ne yan Sanda suka kama biyo bayan wannan tarzoma ta jiya juma’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu