Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 21/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 21/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

An gano akwatunan nadar bayanai jiragen sojin Faransa da suka yi hatsari a Mali

media Hotunan wasu daga cikin dakarun Faransa JEFF PACHOUD / AFP

Rundunar sojin Faransa ta ce an gano akwatunan nadar bayanai na jiragen sojin da suka yi taho mu gana a yankin Liptako da ke daf da iyakar Mali, Nijar da kuma Burkina Faso.

A ranar litinin da ta gabata ne wannan hatsari ya faru, a daidai lokacin da dakarun saman Faransa ke farmaki kan yan ta’adda a yankin na Liptako. To sai dai gano wadannan akwatunan zai taimaka domin sanin hakikanin abin da ya haddasa mutuwar sojojin 13.

Fadar shugaban Faransa ta ce an samu hadarin ne lokacin da jiragen biyu masu saukar ungulu suka yi taho mu gama a tsakanin su.

Wannan shi ne hadari mafi muni da sojojin Faransa suka gamu da shi tun bayan hadarin bama-baman Lebanon na shekarar 1983 wanda ya hallaka mutane 58.

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana kaduwar sa da hadarin wanda ya hada da hafsoshi guda 6 da wadanda ba hafsoshi ba guda 6 da kuma kofur guda da ke aikin yaki da 'yan ta’adda a Sahel.

Ministar tsaro Florence Parly ta ce hadarin ya girgiza rundunar sojin da ma’aikatar tsaro da kasar Faransa baki daya, yayin da ta ce za’a kaddamar da bincike akai domin gano abinda ya yi sanadinsa.

Cikin wadanda hadarin ya ritsa da su harda ‘dan tsohon minista kuma Sanata Jean-Marie Bockel.

Bakwai daga cikin sojojin na aiki ne da runduna ta 5 da ke yaki da jiragen shalkwafta a Pau da ke Faransa, yayin da 4 kuma ke karkashin dakarun Gap.

Gwamnatin Faransa zata gudanar da addu'o'i a fadin kasar ranar litinin mako na sama ,yayinda aka bayyana cewa Ministar tsaron kasar Florence Parly zata kai ziyara kasar Mali nan gaba.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure